Mar 14, 2018 19:15 UTC
  • Isma'ila Haniyyah Ya Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Rami Hamdallah

Shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas Ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa piraministan Palasdinawa a yankin Gaza a jiya Talata.

Haniyyah ya ce; Harin da aka kai, ya shafi dukkanin palasdinawa, don haka wajibi ne a yi riko da hadin kai a matsayin mayar da martani.

Bugu da kari Haniyyah ya bayyana kokarin da jami'an tsaro suke yi domin gano wadanda suka shirya da kuma kai harin.

A jiya Talata ne dai aka kai wa ayarin motocin Piraminstan Palasdinawa Rami Hmadallah hari, ta hanyar tashin bom daga nesa.

A cikin ayarin da aka kai wa harin da akwai shugaban hukumar leken asiri hukumar kwarya-kwaryar Palasdinu, Majid Faraj, dai kuma Husain Sheikh wanda memba ne na babban kwamitin kungiyar Fatah.

Masu gadin Piraministan su shida ne su ka jikkata sanadiyyar hari.

Tags