Amurka Ta Bai Wa HKK Damar Ci Gaba Da Kashe Palasdinawa.
Amurka Ta Bai Wa HKK Damar Ci Gaba Da Kashe Palasdinawa.
Amurka ta yi kafar angulu akan fitar da wani kuduri daga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya akan kisan da Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta yi wa Palasdinawa. Da safiyar asabar ce dai kwamitin tsaron MDD ya yi zama domin tattauna da kuma fitar da bayani akan yadda 'yan sahayoniya su ka murkushe Zanga-zangar lumana ta palasdinawa a ranar tunawa da hakkin komawa kasarsu ta gado. Sai dai Amurka ta nuna kin yardarta da yunkurin, ta kare haramtacciyar kasar Isra'ila ta hana a fitar da kowane irin kuduri.
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres ya bukaci ganin an gudanar da bincike na gaggawa akan abin da ya faru a Gaza a ranar juma'a.
Palasdianwa mazauna yankin Gaza sun fito kwansu da kwarkwatarsu a ranar juma'a domin raya ranar 'kasa' wacce ake tunawa da hakkin palasdinawa na komawa zuwa gidajensu na gado da aka kore su daga cikinsu a yayin kirkirar haramtacciyar Kasar Isra'ila. Kuma tare da cewa gangamin na Palasdinawa na zaman lafiya ne, sojojin haramtacciyar Kasar Isra'ila sun bude wuta tare da kashe mutane 17 da kuma jikkata wasu fiye da 1000.
Wakilin Palasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya, Riyadh Mansur ya bayyana cewa; Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun yi wa palasdinawa kisan kiyashi."
Kisan da aka yi wa mutanen Gaza ya sa duniya tana yin tir da da shi, don haka Kuwaiti ta bukaci da a yi zaman na jiya a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Sai dai duk da hakan, kasar Amurka ta dauki matakan da ta saba a duk lokacin da wani batu mai alaka da haramtacciyar kasar Isra'ila ya taso. Ta hana kwamitin tsaron ya dauki duk wani mataki akan laifukan 'yan sahayoniya.
Amurka ta cika duniya da kurari akan cewa ita mai kare hakkin bil'adama ce kuma tana bayyana cewa hatta yake-yaken da take yi domin wannan manufa ce.
Abin tambaya anan shi ne wane irin dalili Amurkan take da shi na kare laifukan da 'yan sahayoniya suke tafkawa akan palasdinawa?
Daga lokacin da aka kafa haramtacciyar kasar Isra'ila a 1948 zuwa yanzu, Amurka ce kan gaba wajen ba ta kariya ta fuskar soja da kudi. Hatta a karshen mulkin Barrack Obama ya bai wa haramtacciyar kasar Isra'ila kayan yaki na dala biliyan 38. Amma daga zuwan Donald Trump kan mulki ya sake rubanya kariyar da yake bai wa 'yan sahayoniyar. Daga ciki da akwai yadda ya bai wa haramtacciyar kasar Isra'ila birnin Kudus. Haka nan kuma mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Kudus.
Sai dai duk da wannan taimako da kariyar da Amurkan take bai wa 'yan sahayoniyar, dalilai masu yawa suna nuni da cewa babu abin da zai hana faduwa da rushewar haramtacciyar kasar Isra'ila.