Kasashen Iran, Turkiyya Da Rasha Zasu Yi Taro Kan Batun Siriya
Apr 01, 2018 09:56 UTC
Kasashen Iran da Turkiyya da kuma Rasha, zasu yi wani taro domin tattauna wa kan batun Siriya.
Fadar shugaban Turkiya ta fidda wata sanarwa inda ta bayyana cewa, shugabannin kasashe uku za su yi ganawa a Ankara babban birnin kasar Turkiyan, a ranar 4 ga watan nan da muke ciki, domin yin tattaunawa kan batun Syria.
Ko a ranar 22 ga watan Nuwamban bara, shugabannin kasashen Turkiyya, Rasha da Iran sun yi ganawa a birnin Sochi na kasar Rasha, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan yanayin da ake ciki game da batun kasar Siriya, tare da yin kira da a gudanar da cikakken zaman taron neman sulhu kan kasar Syria.
Tags