Ma'aikatan Man Fetir 15 Sun Rasu A Kuweit
Kimanin ma'aikatan man fetir 15 ne suka rasa rayukansu sanadiyar hatsarin mota a kasar Kuweit.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto hukumomin kasar Kuweit na cewa a jiya lahadi wasu manyan motocin Bas-Bas biyu dauke da ma'aikatan kamfanin man fetir na kasar sun yi hatsari a kusancin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar rasuwar ma'aikata 15, bakwai daga cikinsu 'yan kasar Indiya ne.
A nasa bangare Muhamad Basari daga cikin shugabanin kamfanin hako da man fetir na kasar Kuweit din ya yi karin haske a game da mutanan da suka rasa rayukansu, inda ya ce bakwai 'yan kasar Indiya ne, biyar kuma 'yan kasar Masar ne yayin da sauran ukun 'yan kasar Pakistan ne.
Shima a nasa bangare Kanar Khalil Al-Amir kakakin jami'an kwana-kwana na kasar ya ce wadanda suka rasa rayukansu ma'aikan wani kamfanin hako da man fetir mai zaman kansa ne mai suna Burgan Drilling .