Babban Sakataren M.D.Duniya Ya Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Rikicin Siriya
(last modified Sat, 26 Mar 2016 09:45:30 GMT )
Mar 26, 2016 09:45 UTC
  • Babban Sakataren M.D.Duniya Ya Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Rikicin Siriya

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada bukatar ganin an kawo karshen duk wani tashe-tashen hankula musamman ayyukan ta'addanci a cikin kasar Siriya.

A ziyarar da ya gudanar a kasar Lebanon a jiya Juma'a; Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon baya ga ganawar da ya yi da mahukuntan kasar ta Lebanon kuma ya kai ziyarar aiki zuwa sansanin 'yan gudun hijiran kasar Siriya da ke yankin Al-Dalhamiyyah a shiyar arewacin kasar ta Lebanon, inda ya bayyana fatan ganin Majalisar Dinkin Duniya ta kai ga samun nasarar tabbatar da shirin dakatar da bude wuta a Siriya da nufin shawo kan tashe-tashen hankulan kasar.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya kuma ziyarci dakarun Majalisar Dinkin Duniya da suke aikin wanzar da zaman lafiya a kan iyakar kasar Lebanon da haramtacciyar kasar Isra'ila ta {UNIFEL}>