Apr 16, 2018 12:27 UTC
  • Fiye Da Mutane 59,000 Ne Su Ka Koma Gidajensu A Yankin Ghuta Ta Gabas

Cibiyar Sulhu a tsakanin mutanen al'ummar Syria ce ta sanar da komawar mutanen zuwa gidajensu bayan da aka kwace yankin daga 'yan ta'adda

Kamfanin dillancin labarun Mehr ya nakalto majiyar gwamnatin Syrai na cewa; Mutanen sun koma yankin ne bisa kokarin cibiyar sulhu a tsakanin al'ummar Syria.

Babbar shalkwatar sojan Syria ta fitar da bayani a ranar asabar da acikin ta bayyana cewa an 'yantar da dukkanin yankin na Ghuta ta gabas daga hannun 'yan ta'adda. Yankin yana da muhimmanci saboda kusancinsa da birnin Damasucus. "Yan ta'dda da su ka yi tunga a cikinsa sun rika harba wa babban birnin  kasar Syria makamai masu linzami da rokoki.

A wani labarin daga kasar Syria, majiyar soja sun karyata labarin dake cewa 'yan sahayoniya sun ka hari a garin Halab. Majiyar ta ce karar da aka rika ji ta fashewar abubuwa, sojoji ne suke lalata nakiyoyin da 'yan ta'adda su ka dasa kafin ficewarsu daga yankin.

Tags