Pakistan : Taliban Ta Dauki Nauyin Kai Harin Lahore
(last modified Mon, 28 Mar 2016 04:36:21 GMT )
Mar 28, 2016 04:36 UTC
  • hari a Lahore
    hari a Lahore

Wata kungiya daga Taliban mai suna ''Jamaat-ul-Ahrar'' ta dauki alhakin kai harin ta'adancin da yayi sanadin mutuwar mutane da dama galibi mata da yara a birnin lahore na kasar Pakistan.

kungiyar ta ce ta shirya kai harin ne kan mabiya addinin krista.

Hukumomi a wannan kasa sun ce akalla mutane 65 ne kawo yanzu suka rasa rayukansu sakamakon wata fashewa da ta faru a birnin a marecen jiya lahadi, yayin da wasu rahotanni ke cewa adadin rayukan da suka salwanta zai iya wuce hakan.

Majiyoyin gwamnatin lardin sun ce, ko baya ga mamatan akwai wasu mutane sama da 300 da suka samu raunuka sakamakon wannan fashewar data auku gaf da wurin wasan yara inda iyalai da dama suka hadu domin shagulgulan Easter a wurin shakatawar na Gulshane-Iqbal Park.

A halin da ake ciki hukumomin yankin sun bada umurnin rufe dukkan wuraren shakatawa na lardin, tare da ayyana zamen makokin na kwanaki uku.

Tuni dai fadar Vatikan ta fitar da sanarwar yin allawadai da harin.

Wannan dai shi ne harin ta’addanci mafi muni da aka kai a kasar ta Pakistan a cikin watannin baya-bayan nan.