Rikici Na Kara Tsanani Tsakanin Kungiyoyin 'Yan Ta'adda A Siriya
(last modified Sat, 28 Apr 2018 06:40:13 GMT )
Apr 28, 2018 06:40 UTC
  • Rikici Na Kara Tsanani Tsakanin Kungiyoyin 'Yan Ta'adda A Siriya

A ci gaba da rikici tsakanin kungiyoyin 'yan ta'adda a siriya, wani komandan Jaishul-Izza a yankin Idlib ya hallaka .

Tashar Talabijin din Almayadin ta nakalto wata kafar watsa labarai mai alaka da 'yan adawar siriya na cewa a ci gba da rikicin gida tsakanin kungiyoyin 'yan ta'addar Siriya a  jiya juma'a an hallaka Khalid Ma'arati da ake kira da Abu Lahab mataimakin babban komandan kungiyar 'yan ta'adda na Jaishul-Izza a garin Khan Shaihun dake gefen kudancin Idlib.

A bangare guda, kungiyar 'yan ta'addar Ahraru-Sham ta sanar da cewa daga cikin shugaban kungiyar kuma alkali mai suna Abdul...Muhsiny ya tsallaka rijiya da baya bayan wani hari da aka kai masa a arewacin kasar ta Siriya.

A matsayin mayar da martani, kungiyar ta Ahraru-Sham ta dauki matakin hana shige da fice na tsahon kwanaki uku a babban birnin jahar ta Idlib.

A ranar alhamis din da ta gaba tace wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun hallaka Abu-ward Kufur Badikh wani komandan kungiyar Ahraru-Sham da mai gadinsa Abu salim Banash, da kuma Mustapha Haj Ali shugaban bangaren sadarwa na hukumar Ilimin jahar Idlib dake koyon bayan 'yan ta'adda a arewacin jahar.