Ana Kidayar Kuri'u Bayan Zaben 'Yan Majalisa A Labanon
(last modified Mon, 07 May 2018 05:48:21 GMT )
May 07, 2018 05:48 UTC
  • Ana Kidayar Kuri'u Bayan Zaben 'Yan Majalisa A Labanon

An fara kidayar kuri'u zaben 'yan majalisar dokoki na farko tun bayan na shekara 2009, a kasar Labanon.

Saidai ma'aikatar cikin gidan kasar ta ce ba'a samu fitowar jama'a sosai ba a zaben kamar a shekara 2009. 

Sanarwar da ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar ta ce kashi 49 cikin dari ne suka fito zaben na jiya, sabanin kashi 54 cikin dari idan aka kwatanta da waccen lokacin. 

Masharhanta dai na ganin dai babu wata makawa jam'iyyun gargajiya, musamman ta 'yan Hizbullah zasu samu rinjaye a majalisar dokokin mai mambobi 128, amma dai duk ya danganta da irin kawancen da zata kulla ko kuma zata sabunta.

A bangaren fira ministan kasar Saad Hariri kuwa, jam'iyyarsa zata iya rasa wasu kujeru a majalisar, amma hakan ba zai yi wani tasiri ba ga kujerarsa ta shugaban gwamnatin kasar.