Afganistan : Mutane 9 Sun Mutu A wani Harin Ginin Gwamnati
(last modified Sun, 13 May 2018 17:08:19 GMT )
May 13, 2018 17:08 UTC
  • Afganistan : Mutane 9 Sun Mutu A wani Harin Ginin Gwamnati

Rahotanni daga Afganistan na cewa, a kalla mutane tara ne suka rasa rayukansu a wani hari da 'yan bindiga suka kai a wani ginin gwamnati dake yankin Jalalabad a gabashin kasar.

Maharan dai sun kaddamar da harin ne bayan tashin wani bom da aka dana a mota, inda daga bisani suka kusa a cikin ginin suka fara harbe harbe, kamar yadda kakakin gwamna yankin, ya shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP. 

Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu da akwai wasu mutane 36 da suka raunana.

Wadanda harin ya yi ajalisu sun hada da wani jami'in 'yan sanda da wasu fararen hula 8, ciki har da ma'aikatan ma'aikatar ta baitalmali su guda uku, wandanda suka mutu a tashin bom a harabar ma'aikatar.

Tuni dai  kungiya 'yan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kai harin.

Wannan harin dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu jerin hare hare da aka kai a wani ofishin 'yan sanda a Kabul babban birnin kasar, inda mutane goma suka rasu, wanda na farkon kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kaiwa, sai na biyu wanda Taliban ta ce ita keda alhakin kaisa.