Hare-Haren Ta'addanci Sun Lashe Rayukan Fararen Hula A Kasar Iraki
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i3106-hare_haren_ta'addanci_sun_lashe_rayukan_fararen_hula_a_kasar_iraki
Wasu hare-haren ta'addanci biyu sun lashe rayukan mutane masu yawa a birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki a yau Talata.
(last modified 2018-08-22T06:58:03+00:00 )
Mar 29, 2016 06:06 UTC
  • Hare-Haren Ta'addanci Sun Lashe Rayukan Fararen Hula A Kasar Iraki

Wasu hare-haren ta'addanci biyu sun lashe rayukan mutane masu yawa a birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki a yau Talata.

Rahotonni sun bayyana cewa: Wani bom ya tarwatse a tsakanin leburori da suke taruwa da safe domin neman aikin yi a yankin Babul-Sharki da ke birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki a safiyar yau Talata lamarin da ya janyo hasarar rayukan mutane akalla 8 tare da jikkatan wasu fiye da 25.

Har ila yau wani bom ya tashi a dandalin Dairan da ke birnin na Bagadaza a safiyar yau Talata lamarin da ya janyo hasarar rayukan fararen hula, sai dai har yanzu babu rahoton irin hasarar rayukan da aka yi.

Tun a shekara ta 2014 ne kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta mamaye garuruwa masu yawa a yankin arewa maso gabashin kasar Iraki, inda mayakanta suke ci gaba da aiwatar da kisan killa kan al'ummar kasar.