Afganistan : An Kai Hari A Ma'aikatar Cikin Gida
May 30, 2018 10:53 UTC
Rahotanni daga Afganistan na cewa wasu 'yan bindiga hudu sun kai hari a ma'aitakar cikin gidan kasar, a yau Laraba.
Bayanai sun ce an yi ta musayar wuta, da kuma jin tashin fashewar abubuwa masu karfin gaske a harabar ma'aikatar.
kakakin ma'aikatar cikin gidan kasar, Najib Danish, ya shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, da farko wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa kafin daga bisani an yi ta harbe harbe.
Har zuwa lokacin gabatar da wadannan labaren babu karin bayyani akan barna ko kuma hasara ta rayuka ko jikkata da aka samu a wanann harin.
Tags