Kasashen Syria Da Algeria Sun Kudiri Aniya Kara Bunkasa Alakarsu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i3151-kasashen_syria_da_algeria_sun_kudiri_aniya_kara_bunkasa_alakarsu
A ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Syria Walid Mu'allim yake gudanarwa a kasar Algeriya bangarorin biyu sun jadda aniyarsu ta ci gaba da kara fadada alakarsu.
(last modified 2018-08-22T06:58:03+00:00 )
Mar 30, 2016 05:36 UTC
  • Kasashen Syria Da Algeria Sun Kudiri Aniya Kara Bunkasa Alakarsu

A ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Syria Walid Mu'allim yake gudanarwa a kasar Algeriya bangarorin biyu sun jadda aniyarsu ta ci gaba da kara fadada alakarsu.

Kamfanin dillancin labaran SANA ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da ministan harkokin wajen kasar ta Syria Walid Mu'allim yake ganawa da Firayi ministan kasar Algeriya Abdulmalik Salal a jiya a birnin Algiers, bangarorin biyu sun jadda wajabcin ci gaba da kara bunkasa alaka a dukkanin bangarori a tsakanin kasashensu.

Kasar Algeriya na daya daga cikin kasashen larabawa da ba su amince da salon siyasar da wasu kasashen larabawan suka dauka ba kan kasar Syria, musamman ma Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa gami da Bharain, wadanda suke daukar nauyin kungiyoyin 'yan ta'adda kai tsaye domin yaki da gwamnatin Syria.