Dakarun Hashadu Sha'abi Sun Kai Hari Kan Ciboyoyin Da'esh A Siriya
Dakarun sa kai na kasar Iraki dake yiwa lakabi da hashadu Sha'abi sun kai hari kan wasu wuraren mayakan kungiyar ISIS a kasar Siriya
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto kafar watsa labaran Furata News na cewa a wani farmaki da dakarun sa kai na kasar Iraki suka kai jiya laraba, sun fatattaki mayakan Da'esh da suka yi kokarin kusantar kan iyakar kasar daga cikin kasar Siriya.
A ranar 7 ga wannan wata na yuni da muke ciki wani jiragen yakin Iraki samfarin F-16 ya kai hari kan maboyar 'yan ta'addar ISIS a cikin kasar ta Siriya,kafin hakan dai a ranar 25 ga watan Mayun da ya gabata wadanan jirage sun kaddamar da hare-hare kan wuraren 'yan ta'addar na ISIS da kuma ma'ajiyar makamansu a yankin Hijan na kasar Siriya bisa umarnin Piraminista Haidar Abadi.
Rawar da kungiyar sa kai na Hashadu sha'abi suka taka a yaki da 'yan ta'adda ISIS a Iraki ya taimaka wajen korar 'yan ta'addar na ISIS daga cikin kasar ta Iraki.