Iraki : Kotun Tsarin Mulki Ta Soke Zaben 'Yan Majalisa
Kotun koli mai kula da tsarin mulki a Iraki, ta bada umurnin sake kidayar kuri'un da aka kada da hannu a zaben majalisar dokokin kasar na ranar 12 ga watan Mayu da ya gabata.
Za'a dai kwashe makwanni da dama ko kusan wata guda ma ana kidayer kuri'in, a daidai lokacin da kuma wa'adin 'yan majalisar dokokin ke kawo karshe a hukumance a ranar 30 ga watan Yunin nan.
Sake kidayar dai zata shafi daukacin kuri'u kimanin Miliyan 11 da aka kada ciki har da na kasahen waje a zaben da tunda farko aka bayyana dan takara Moqtada Sadr ya lashe.
Tunda farko dai majalisar dokokin kasar ta bukaci da soke zaben na bangaren 'yan kasashen waje da jami'an tsaro da kuma 'yan gudun hijira, a inda nan ne mafi yawa aka samu kura kurai da kuma zargin magudi, a zaben da aka gudanar a karon farko ta hanyar na'ura.