Jun 27, 2018 12:28 UTC
  • Kungiyar Palasdinawa Ta Hamas Ta Yi Gargadin Maida Martani Kan Hare-Haren Sojin H.K.Isra'ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da ke Palasdinu ta fitar da sanarwar cewa: Kungiyar zata dauki matakan maida martani kan hare-haren wuce gona da irin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kaddamarwa kan al'ummar Palasdinu.

A sanarwar da kakakin kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas Fauzi Bourham ya fitar ya jaddada cewa: Kungiyoyin gwagwarmayar Palasdinawa ciki har da Hamas suna cikin shirin ko-ta kwana kuma zasu ci gaba da yin aiki da hakkin da ya rataya a wuyarsu na kare al'ummar Palasdinu tare da maida martani kan duk wani harin wuce gona da irin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

A safiyar yau Laraba jiragen saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hari kan wata motar Palasdinawa a sansanin al-Nusairat da ke yankin Deir Balah. Kamar yadda a jiya Talata jiragen saman yakin na sojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai hare-hare kan yankunan arewa da kuma gabashin Zirin Gaza.

 

Tags