Syria: 'Yan Ta'adda Da Dama Sun Mika Makamansu Ga Gwamnati
Shugaban cibiyar sulhu a kasar Syria, Janar Alaxy Tisigankov ya ce; Masu dauke da makamai 250 ne suka mika makaman nasu ga sojojin gwamnati
Tashar talabijin din "Rusiyal-Yaum" wacce ta ba da labarin ta ci gaba da cewa; Mutanen sun fito ne daga cikin kauyuka guda uku da su ne; Umma-Walad, Abdha', da Habib.
A halin da ake ciki a yanzu, sojojin Rasha suna shiga tsakanin tattaunawar da ake yi a tsakanin Sojojin kasar Syria da 'yan ta'adda a garin Dar'aa.
Janar Tisigankov ya kara da cewa; Daga cikin makaman da mutane su ka mika da akwai bindigogi 118 da kuma wasu kayan aikin soja masu girma.
A wani labarin na daban, mayaka a cikin kauyuka 9 a gundumar Dar'aa sun mika makamansu ga sojojin gwamnatin kasar.
A cikin kwanakin bayan nan sojojin Syria sun shelanta yaki akan 'yan ta'adda da suke a gundumar Dar'aa domin fitar da su daga cikinsa.