Dakarun Iraki Sun Ragargaza Wasu Sansanoni 2 Na 'Yan Ta'addan ISIS
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32152-dakarun_iraki_sun_ragargaza_wasu_sansanoni_2_na_'yan_ta'addan_isis
Dakarun gwamnatin Iraki gami da sauran dakarun sa kai na al'ummar kasar sun samu nasarar ragargargaza wasu sansanoni biyu na 'yan ta'addan Daesh a arewacin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:02:03+00:00 )
Jul 01, 2018 08:44 UTC
  • Dakarun Iraki Sun Ragargaza Wasu Sansanoni 2 Na 'Yan Ta'addan ISIS

Dakarun gwamnatin Iraki gami da sauran dakarun sa kai na al'ummar kasar sun samu nasarar ragargargaza wasu sansanoni biyu na 'yan ta'addan Daesh a arewacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Mehr ya habarta cewa, mai magana da yawun rundunar sojin kasar Iraki Manja janar Yahya Rasul ya sanar da cewa, dakarun kasar gami da dakarun sa kai sun samu nasarar tarwatsa wasu sansanonin 'yan ta'addan takfiriyya na Daesh a yankin Samirra da ke cikin gundumar salahdin a rewacin kasar.

Ya ce sun kame wasu da dama, an kuma halaka wasu, yayin da wasu kuma suka mika kansu da makaman da ke hannunsu.

A ranar Alhamis da ta gabata a an rataye wasu 'yan ta'adda 12 da suke da hannu a kisan da ake yi wa al'ummar Iraki.