Yahudawan Sahyuniya Sun Fara Rusa Wasu kauyukan Falastinawa A Gabashin Quds
Jami'an Tsaron Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun fara rusa wasu kauyukan Falastinawa a yankunan da ke gabashin birnin Quds.
Rahotanni daga Palestine sun habarta cewa, a ci gaba da hankoron mamaye yankunan Falastinawa da Isra'ila ke, a yau jami'an tsaro da motocin budoza sun rusa gidaje da dama na falastinawa a gabashin birnin Quds.
A waje daya kuma kamfanin dillancin labaran Palestine ya habarta cewa, wasu yahudawan sahyuniya yan share wuri zauna sun kutsa kai a cikin masallacin mai alfarma.
Daruruwan jami'an tsaron Isra'ila ne a cikin kayan sarki suke bayar da kariya ga yahudawan a lokacin da suka kutsa kaia cikin masallacin tare da keta alfarmarsa.
Tun daga farkon watan Yunin da ya gabata ya zuwa yanzu, Haramtacciyar kasar Isra'ila ta kame falastinawa 355, da nufin murkushe boren baya-bayan nan da suka fara, domin neman hakkin Falastinawa na komawa Palastine, bayan da aka tilasta su yin hijira shekaru fiye da arbain da suka gabata zuwa kasashe makwabta.