Syria: An Kashe Manyan Kwamandojin 'Yan Ta'adda Biyu
Jul 06, 2018 13:02 UTC
A yau Juma'a me majiyar kungiyar 'yan ta'adda ta Syrian Free Army ta sanar da kashe kwamandojinta biyu a kudancin kasar Syria
Kungiyar ta ce kwamandojin da aka kashe su ne Muhammad al-mahamid da Muhammad Kasim al-kasur al-hariri a kusa da garin al-Nu'aimah da ke gabacin birnin Daraa.
A gefe daya, sojojin kasar ta Syria sun rusa sansanin karshe da yake a karkashin ikon kungiyar 'yan ta'adda ta al-Nusrah a garin al-Nu'aimah a gabacin Daraa.
Bugu da kari sojojin na Syria sun fatattaki da kuma kashe 'yan ta'adda daga garuruwan al-Nuaimah da kuma MAzariu al-shariyyah.
Sojojin Syria sun fara kai farmaki akan 'yan ta'adda da suke a yankin Daraa mai iyaka da kasar jOrdan.
Tags