Tashin Bam Ya Hallaka Mutane 18 A Siriya
Wata Mota shake da bama-bamai ta tarwatse a gefen gabashin jihar Dairu-Zur dake gabashin Siriya, lamarin da ya yi sanadiyar salwantar rayukan mutane 18
Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa lamarin ya auku ne a kauyen Basira na gefen gabashin jihar Dairu-Zur, inda wani komandan dakarun kurdawa tare da masu mara masa baya 10 da kuma wasu fararen hula 7 suka rasa rayukansu.
Ya zuwa yanzu babu wani gungu ko kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari.
Dakarun Kurdawan Siriyan dai na samun goyon bayan Amurka, kuma daga ranar 17 ga watan Oktoban 2017 bayan janyewar mayakan kungiyar ISIS daga garin Rakka, suka karbin jagorancin garin.
Wannan Dakaru dake samun goyon bayan Amurka da kawanta wajen kai hare-hare, sun fadada yankunan da suka mamaye a gabashi da arewa maso gabashin Siriya a jahohin Rakka da Dairu-Zur.