An Gano Wasu Manyan Kabarurruka Makare Da Jama'a A Kasar Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32415-an_gano_wasu_manyan_kabarurruka_makare_da_jama'a_a_kasar_siriya
Kwamitin sake gina garin Raqqa da ke gabashin kasar Siriya ya sanar da cewa: An gano wasu manyan kabarurruka guda uku dauke da daruruwan gawawwakin mutane da aka aiwatar da kisan gilla kansu a garin na Raqqa.
(last modified 2018-08-22T11:32:08+00:00 )
Jul 21, 2018 12:02 UTC
  • An Gano Wasu Manyan Kabarurruka Makare Da Jama'a A Kasar Siriya

Kwamitin sake gina garin Raqqa da ke gabashin kasar Siriya ya sanar da cewa: An gano wasu manyan kabarurruka guda uku dauke da daruruwan gawawwakin mutane da aka aiwatar da kisan gilla kansu a garin na Raqqa.

A bayanin da kwamitin sake gina garin Raqqa na kasar Siriya ya fitar  ya bayyana cewa: Bayan tsarkake garin Raqqa daga mamayar 'yan ta'addan kungiyar Da'ish an gano manyan kabarurruka gusda uku dauke da gawawwakin mutane 1,236, kuma akwai yiyuwar sake gano wasu tarin kabarurrukan.

A gefe guda kuma sojojin gwamnatin Siriya da dakarun sa-kai na kasar sun samu nasarar yantar da kauyuka biyar da suke lardin Quneitra da ke kudancin kasar Siriya.