Siriya : Harin IS Ya Yi Ajalin Mutum 54
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32473-siriya_harin_is_ya_yi_ajalin_mutum_54
Kungiyar 'yan ta'adda ta IS, ta kashe mutum 54 a wasu jerin hare haren kunan bakin wake data kai a wasu kyauwuka dake kudancin Siriya.
(last modified 2018-08-22T11:32:09+00:00 )
Jul 25, 2018 11:04 UTC
  • Siriya : Harin IS Ya Yi Ajalin Mutum 54

Kungiyar 'yan ta'adda ta IS, ta kashe mutum 54 a wasu jerin hare haren kunan bakin wake data kai a wasu kyauwuka dake kudancin Siriya.

Wannan dai su ne hare hare mafi muni da kungiyar ta kai a kasa a watanni da dama a wannan kasa ta Siriya dake fama da yaki.

An dai kai hare haren ne a lardin Sueda dake karkashin ikon sojojin gwamnatin Bashar Al'Assad, inda 'yan kunan bakin wake hudu suka tarwatsa kansu a wannan safiyar ta Laraba.

Bayanai daga kafofin yada labarai na gwamnati sun ce sojojin kasar sun kai hare haren jiragen sama don maida martani kan 'yan ta'addan.