Harin IS Ya Kashe Mutum 30 A Yayin Zaben Pakistan
Jul 25, 2018 11:05 UTC
Rahotannin daga Pakistan na cewa mutane a kalla talatin ne suka rasa rayukansu, kana wasu 30 kuma na daban suka raunana a wani harin kunar bakin wake da aka kai a kusa da wata runfar zabe dake lardin Qetta a kudu maso yammacin kasar.
Harin dai ya auku ne a daidai lokacin al'ummar kasar ke kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokoki a yau Laraba.
Tuni dai kungiyar 'yan ta'adda ta IS ko Da'esh ta fitar da wata sanarwa a ashafin yada farfaganta na Amaq cewa ita ce ke da alhakin kai harin.
Bayanai sun ce an kai harin ne jim kadan bayan wani harin gurneti a wani ofishin zabe a lardunan Khuzdar da Baloutchistan, inda wani jami'in yan sanda guda ya mutu, wasu uku kuma suka raunana.
Tags