Ci Gaba Da Zanga-zanga A Fadin Kasar Iraki
(last modified Sat, 28 Jul 2018 08:31:57 GMT )
Jul 28, 2018 08:31 UTC
  • Ci Gaba Da Zanga-zanga A Fadin Kasar Iraki

A jiya juma'a da marece al'ummar Iraki sun gudanar da Zanga-zanga a fadin kasar domin nuna kin amincewa da cin hanci da rashawa

Masu Zanga-zangar sun kuma rika bayar da taken nuna kin yardarsu da tabarbarewar aubuwan more rayuwa.

A birnin Bagadaza masu Zanga-zangar sun taru a babban dandalin Tahrir sai dai jami'an tsaro sun hana su shiga cikin yankin "Green Area' da nan ne cibiyar gwamnatin kasar.

Daga birnin Basara ne a kudancin kasar, aka fara gudanar da Zanga-zanga domin nuna kin yarda da yawan dauke wuta da karancin ruwan sha, haka nan rashin aikin yi a tsakanin samari,musamman wadanda su ka kammala jami'a.

A wasu garuruwan na Iraki an sami yin taho mu gama da jami'an tsaro wanda ya kai ga mutuwar biyu daga cikin masu Zanga-zangar.

Tuni da Fira ministan kasar Haydar Abadi ya bayar da umarni a warware matsalolin da al'ummar kasar suke fuskanta.