An Kai Hari A Wani Ofishin 'Yan Gudun Hijira A Afganistan
Jul 31, 2018 11:17 UTC
Rahotanni daga Afganistan na cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani ofishin kula da 'yan gudun hijira dake birnin Jalalabad a gabashin kasar.
Bayanai daga hukumomin yankin sun cewa an samu fashewar wasu abubuwa har sau biyu a safiyar wannan Talata.
Wasu rahotanni sun ce ana ci gaba da kai hari, lamarin da ya sa har yanzu ba'a samu cikakun bayanai ba, amma an samu mutum takwas kawo yanzu da suka jikkata.
An dai kai harin gabanin wani taro da ofishin kula da 'yan gudun hijirar zai yi da abokan huldarsa na kasa da kasa.
Tags