Iraki : An Soke Dokar Biyan Tsaffin 'Yan Majalisa Kudaden Fansho
Kotun kolin Iraki, ta soke dokar nan da 'yan majalisar dokokin kasar suka amince da ita, ta biyan tsaffin 'yan majalisar kudaden ritaya ko fansho.
Kotun dai ta soke dokar biyan kudaden har sai an fitar da wani kudiri kan dokar.
Fira Ministan kasar Haider al-Abadi, ne dake fuskantar boren jama'ar kasar ya mika wannan batu ga kotun kolin ta Bagadaza.
Kafin hakan dai an dai shafe kusan wata guda ana bore a kasar kan yadda gwamnati ke bacaka da kudade.
Su dai 'yan majalisar dokokin Iraki, a lokacin wa'adinsu na shekaru hudu, na karbar albashi na sama da Dalar Amurka 10,000 kuma bayan sun yi ritaya suka karbi kudaden fansho na Dalar Amurka 8,000 a daidai lokacin da wasu 'yan kasar ke cewa su ba su ga komai ba dangane da albarkatun arzikin man fetur din da Allah ya hore wa kasar.