Jiragen Yakin Isra'ila Sun Kaddamar Da Hare-Hare A Zirin Gaza
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32629-jiragen_yakin_isra'ila_sun_kaddamar_da_hare_hare_a_zirin_gaza
A yau jiragen yakin Isra'ila sun kaddamar da hare-hare a kan wasu yankuna na zirin Gaza.
(last modified 2018-08-22T11:32:12+00:00 )
Aug 04, 2018 19:09 UTC
  • Jiragen Yakin Isra'ila Sun Kaddamar Da Hare-Hare A Zirin Gaza

A yau jiragen yakin Isra'ila sun kaddamar da hare-hare a kan wasu yankuna na zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, jiragen yakin na Isra'ila sun harba makamai masu linzami a arewacin yankin zirin Gaza a yau.

Mai magana da yawun rundunar sojin IsrailaAfikhai Ardai ya ce sun kaddamar da hare-haren a kan wasu matasa da suke harba balon-balon da ke dauke da wuta zuwa matsugunnan yahudawa da ke kusa da yankin zirin Gaza.

Babu wasu bayanai daga mahukunta a Gaza kan asarar da aka samu sakamakon hare-haren na yau da jiragen yakin Isra'ila suka kai a yankin.