Sayyid Nasarallah: Kungiyar Hizbullah Ta Fi HKI Karfi
(last modified Wed, 15 Aug 2018 18:57:46 GMT )
Aug 15, 2018 18:57 UTC
  • Sayyid Nasarallah: Kungiyar Hizbullah Ta Fi HKI Karfi

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanan Sayyid Hassan Nasarallah ya ce nasarar da kungiyar ta samu a yakin shekara ta 2006 kan HKI nasarce daga Allah, Majalisar dinkin duniya, kungiyar kasashen larabawa kosa sauran kungiyoyin kasa da kasa basa da hannu a cikin wannan nasarar.

Tashar talabijin ta al-manar ta kasar Labanan ta nakalto shugaban kungiyar yana fadar haka a jiya da yamma a lokacinda yake jawabi a bikin cika shekaru 12 da samun nasara kan HKI a yakin kwanaki 33 a shekara ta 2006.

A wani bangare na jawabinsa sayyid nasarrah ya bayyana cewa JMI zata gudanar da bikin cika shekaru 40 da samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar duk tare da takunkuman da gwamnatin kasar Amurka ta donara mata da nufin tabarbarar da alamura a kasar kafin karshen wannan shekara.

Daga karshe shugaban kungiyar ta Huzbulla ya kamma da cewa a halin yanzu kasashen Amurka da HKI da kuma sauran kawayenta a yankin gabas ta tsakiya sun tabbatar da cewa ba za su taba samun nasara a kan kawance kungiyoyi sa kasashen masu gwagwarmaya a yankin ba.

A jiya 14 ga watan Augusta ne ake cika shekaru 12 da nasarar da kungiyar ta Huzbullah ta samu a yakin da HKI ta kaiwa kasar Labanon da nufin shafe kungiyar kwatakwata a kasar.