Banki Moon:Magance rikicin Siriya ba ya bukatar matakan Soja
A Yayin Taron tattaunawa kan samar da hanyar magance matsalar 'yan gudun hijrar Siriya dake gudana a birnin Geneva na kasar Suizilland Baban saktaren Majalisar Dinkin Duniya ya ce Magance rikicin Siriya ba ya bukatar matakan Soja
Yayin da yake Jawabi a daren jiya Assabar Banki Moon ya ce Halartarmu a birnin Ganeva domin bincike kan halin da 'yan gudun hijrar Siriya ke ciki, mu kuma magance babbar matsalar 'yan gudun hijra da hakan ba zai tabbatu ba sai da samun goyon baya na musaman ga kasashen dake cikin wannan zaure tare kuma da samu goyon bayan kasashen Duniya.
Babban saktaren MDD ya kara da cewa A yanzu mun kwashe sama da shekaru biyar kan wannan batu, lamarin da ya sanya 'yan kasar ta Siriya suka yanke kyakkyawan fatar da suke da shi, amma duk da hakan Duniya za ta ci gaba da kokarin da ta ke yi wajen magance matsalar siriyar da kuma ta 'yan gudun hijra.
Banki Moon ya ce an samu ci gaba a tattaunawar da aka yi kan batun 'yan gudun hijra watan jiya a birnin London domin haka za a ci gaba a kan wannan lamari domin samar da mafitar ta karshe.ko shakka babu kasashen dake makwabtaka da Siriyan sun garbi 'yan gudun hijrar da suka fice kima misali kasar Lobnon ta karbi 'yan gudun hijra sama da million 4, kuma Duniya ta yaba tare da kawo bayan ta ga kasar ta Lobnon
A karshe Banki Moon ya ce ba za a iya magance rikicin siriya da matakan soja ba, babu wata mafuta wajen magance rikicin face ta hanyar tattaunawa , wajibi ne Duniya ta kara kokarin da take yi domin magance matsalar.