Irak: Harin Ta'addanci Ya Ci Rayukan Mutane Da Dama
Rahotanni daga Iraki sun ce an kai harin ne da wata mota da aka makare da abubuwa masu fashewa a garin Tikrita da ke arewa maso yammacin birnin Bagadaza.
Kakakin ma'aikatar lafiya ta Iraki Saif al-badar, ya shaida wa tashar talabijin din Sumariyyah News cewa; Harin na garin Hujjaja ya ci rayukan fararen hula biyar da kuma jikkata wasu mutane 37
Tuni sojojin kasar ta Iraki su ka killace yankin da lamarin ya faru, yayin da aka dauki wadanda su ka jikkata zuwa asibiti.
A kauyen Kunaidhara eda ke arewacin kasar wani bom da aka dasa a gefen hanya ya lalata wata motar farar hula, yayin da ya jikkata wasu mutane biyu.
A shekarar 2017 da ta gabata ne dai gwamnatin Iraki ta sanar da kawo karshen kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh wacce ta kafa iko a wasu sassan kasar da suka hada da kasar Syria. Sai dai har yanzu gyauron kungiyar na ci gaba da kai hare-hare daga lokaci zuwa lokaci.