Sojojin Isra'ila Sun Harbe Falastinawa Biyu A Zirin Gaza
A ci gaba da gudanar da gangamin neman hakkokin Falastinawa da aka kora daga kasarsu domin dawowa gida da dubban Falastinawa suke gudanarwa a zirin Gaza, sojojin Isra'ila sun bude wuta a kan masu gangamin tare da kashe biyu daga cikinsu da kuma jikkata wasu da dama.
Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, kwamitin da ke kula da shirya gangamin hakkin komawar Falastinawa kasarsu ta haihuwa daga wuraren da aka tilasta su tafiya gudun hijira ya sanar da cewa, tun kafin a fara gangamin, daruruwan sojojin yahudawan Isra'ila ne suka yi dandazo a kan shingayen da suka raba su da yankin zirin Gaza.
Daga bisani sojojin yahudawan sun fara harba hayaki mai sanya hawaye, kafin daga bisani su fara yin amfani da harsasan bindiga masu rai a kan dubban fararen hula da suka taru a wurin gangamin da ake gudanarwa cikin lumana.
Yau dai ita ce rana ta ashirin da biyar da ak egudanar da wannan gangami, wanda aka fara tun daga ranar 30 ga watan Maris da ya gabata, wanda ya zuwa yanzu Isra'ila ta kashe falastinawa 180 da suke halartar wannan gangami tun daga lokacin fara shi, tare da jikkata wasu fiye da dubu 19 na daban.