Michel Aoun: Shigar Hizbullah A Syria Bai Saba Wa Ka'ida Ba
Sep 26, 2018 07:01 UTC
Shugaban kasar Lebanon Michel Aoun ya bayyana cewa, shigar mayakan kungiyar Hizbullah a cikin kasar Syria bai saba wa ka'ida ba.
A zantawarsa da mujallar Le Figaro ta kasar Faransa a jiya, shugaban kasar Lebanon Michel Aoun ya bayyana cewa, shigar da kungiyar Hizbullah ta yi a cikin yakin kasar Syria bai saba wa wata doka ko ka'ida ba.
Shugaban na Lebanon ya ce Hizbullah ta shiga kasar Syria ne domin yaki da 'yan ta'adda wadanda suke yin barazana ga tsaron kasar Lebanon da Syria, kuma ta shiga Syria ne bisa gayyatar gwamnatin kasar ta Syria domin yaki da 'yan ta'adda.
Daga karshe ya ce ko shakka babu bayan gamawa da 'yan ta'adda a Syria, kungiyar Hizbullah za ta fice daga kasar.
Tags