Sojojin Syria Sun Kwace Al-Qaryatayn
Sojojin Syria na ci gaba da samun galaba a kokarin da suke na kwace daukacin yankunan dake hannun 'yan ta'adan (ISIS), inda ko a wannnan Lahadin sojojin sunyi nasara kwace birnin Al-Qaryatayn.
Wannan birnin dai na daga cikin yankuna na karshe da 'yan ta'adan sukayi kaka gida a tsakiyar kasar, kamar yadda gidan talabijin din kasar ya rawaito.
Dama kafin hakan kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar OSDH , ta ce dakaraun kasar sun kwace rabin iko da wannan birnin aman ta ce har yanzu ana ci gaba da gwabza fada a wannan yankin.
Idan ana iya tunawa a kasa da wata guda ne dakarun kasar ta Syria suka kaddamar da farmakin kwato duk duk yankunan dake hannun 'yan ta'adan da suka hada mahiman wurin nan mai tarihi na Palmyra da kuma Al-Qaryatayn dukkan nin su biranen dake yankin Homs, kuma a ranar 27 ga watan daya gabata suka kwace ikkon Palmyra.
Bayanai daga kasar dai sun ce yanzu haka dai lardin Sokhné ne dake nissan kilomita 70 daga arewacin Palmyra yayi wa sojojin kasar saura a cikin hannun 'yan ta'adan a yankin na Homs.