Oct 11, 2018 07:48 UTC
  • UNICEF : Kananan Yara A Yemen Na Fuskantar Hadarin Yunwa

Hukumar tallafa wa kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta sanar da cewa, kananan yara a kasar Yemen suna cikin mawuyacin hali na rashin abinci mai gina jiki.

Kamfanin dillancin labaran Anatoly ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da UNICEF ta fitar, ta bayyana cewa kusan dukkanin kananan yara a kasar Yemen suna cikin hadarin mutuwa, sakamakon mummunan halin da suke ciki.

Bayanin na UNICEF ya kara da cewa, sakamakon hare-haren da jiragen yakin kawancen Saudiyya ke kaddamarwa a kan al'ummar kasar ta Yemen, hakan ya yi sanadiyyar rushewar mafi yawan abubuwan da al’ummar kasar ke bukata domin rayuwa.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, a halin yanzu yunwa ita ce babbar barazana ga al’ummar kasar Yemen, musamman kananan yara, wadanda a halin yanzu suke mutuwa saboda rashin abinci, ga kuma kwalara, da sauran cututtuka masu hadari da suke lakume rayukan kananan yara.

Tags