Sayyid Hasan Nasrullah: Trump Cikin Cin Mutumci Yake Kwasar Ganima
(last modified Fri, 12 Oct 2018 19:15:54 GMT )
Oct 12, 2018 19:15 UTC
  • Sayyid Hasan Nasrullah: Trump Cikin Cin Mutumci Yake Kwasar Ganima

Babban Saktaren Kungiyar Hizbullah ta Kasar Labnon ya ce Gwamnatocin Amurka da suka gabata cikin siyasa da mutunci kuma a bayan fage suke kwasar ganima, amma shi kuma Donal Trump a bayyane kuma cikin cin mutunci yake kwasar tashi ganimar.

A cikin jawabin da ya yi a marecen wannan ta juma'a, wajen taron juyayi na mutuwar Amina Salamat ma'aifiyar Shahid Imad Mugniya daya daga cikin kwamondojin kungiyar Hizbullah, sayyid Hasan Nasrullah ya yi ishara kan yadda Shugaban kasar Amurka Donal Trump ke tatsar mahukuman Saudiya yana mai cewa kamata ya yi shugabanin kasashen Larabawa su dauki darasi daga fircin Donal Trump kan kasar Saudiya inda ya sha nanata cewa in ba dan Amurka ba gwamnatin Saudiya ba za ta iya mako guda, ba tare da rushe ba.

hasan Nasrullah ya ce abin mamaki ga yarima mai jiran gado babu wani mai martayi da ya mayarwa shugaban kasar ta Amurka face murmushi da kuma shuru kan cin mutunci da ake yi musu.

Babban Saktare kungiyar Hizbullah ya ce Jamhoriyar musulinci ta Iran ba ta taba daukan irin wannan cin mutunci ba kuma ba ta wasa a game hukuncin kasar ta ba, shi kansa Trump ya yarda da irin karfin da take da shi a yankin gabas ta tsakiya, inda ya ce cikin awa 12 kasar ta Iran na iya mamaye yankin.

Sayyid Nasrullah ya ce manufar Donal trump shine tsoratar da wasu kasashen yanki na sayan makaman yaki masu yawa a wajen Amurka, sannan kuma ya bukaci hukumomin yankin gabas ta tsakiya da su sasanta da Al'ummarsu sannan kuma su yi kokari wajen magance matsalolinsu.

Yayin da ya koma kan da'awar Piraministan HK isra'ila Benjmin Natanyahu da ya ce Kungiyar Hizbullah ta tara tarin makamai a kusa da filin tashin jiragen birnin Bairout, Sayyid Nasrullah ya ce matakin da ministan harakokin wajen kasar ya dauka na nuna wa wakilan kasashen Duniya wurin ya kara bayyana karerakin Natanyahu a fili.