Kashoggi : An Fara Binciken Ofishin Jakadancin Saudiyya
Hukumomin Turkiyya sun sanar da fara bincike a karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake Santanbul kan batun bacewar dan jaridan nan Jamal Kashoggi.
Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa akwai yiyuwar an kashe dan jaridan.
Kafofin yada labarai daga Turkiyya sun nuno hotunan ayarin wasu motoci guda shida cikin kwararen matakan tsaro sun isa ofishin jakadancin Saudiyyar a kimanin karfe 7:00 na yamma ogogon wurin, inda 'yan sanda wasu sanye da kaki da kuma wasu da farin kaya suka shiga ofsihin domin fara binciken.
Kafin hakan dai a cewar labarin wasu jami'an Saudiyya da za'a hadin gwiwa dasu a binciklen sun isa ofishin sa'a guda kafin 'yan sandan Turkiyya su iso.
An dai fara wannan binciken kwana guda bayan wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaba Recep Tayyip Erdogan, na Turkiyyar da Sarki Salmane na Saudiyyar inda suka tattauna kan batun bacewar dan jaridan Kashoggi yau sama da mako biyu da suka gabata bayan shigarsa ofishin jakdancin na Saudiyya da bai sake fitowa.
Tunda farko dai 'yan sanda Turkiyya sun yi zargin an kashe dan jaridan, batun da Saudiyyar ke ci gaba da musuntawa.