Oct 24, 2018 05:55 UTC
  • Wakilin Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin Siriya, Staffan de Mistura
    Wakilin Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin Siriya, Staffan de Mistura

A wani lokaci yau Laraba ake sa ran wakilin Majalisar Dinkin Duniya kan Siriya, Staffan de Mistura zai kai wata ziyara a Damascos fadar mulkin kasar Siriya, domin tattauna hanyoyin kafa wani kwamiti na girka wani sabon kundin tsarin mulki.

Sanarwar da MDD ta fitar ta ce Di Mistura zai je Siriyar ne bisa gayyatar mahukuntan kasar, amma bata fayyace ba ko shugaba Bachar Al-Assad na na daga cikin manyan jami'an kasar da wakilin na MDD zai gana dasu ba.

Kasashen yamma dai sun bukaci Stafan di Mustura da ya gaggauta kafa kwamitin da zai duba hanyoyin da 'yan Siriya zasu bi don girka wani sabon kundin tsarin mulki

An bayyana cewa kwamitin zai kunshi mambobi 150, da suka hada da wakilai 50 daga bangaren gwamnati, da 50 daga bangaren 'yan adawa da kuma wasu 50 daga wakilin MDD wanda shi kuma zai hada da kwararau da kuma wakilian kungiyoyin fararen hula.

Mambobi 15 ne dai daga cikinsu za'a dora wa yaunin rubuta sabon kundin tsarin mulkin kamar yadda MDD ta tsara, saidai gwamnatin Damascos bata gamsu ba da jerin sunayen da MDD ta gabatar ba. 

Tags