Kawo Karshen Da'esh Shi Ne Babbar Manufar Sabuwar Gwamnatin Iraki
Sabon firaiministan kasar Iraqi "Adil Abdul-MaHdi" a ganawarsa da wasu jami'an sojojin kasar ta kuma wasu manya-manyan jami'an tsaro a ranar Asabar da ta gabata, ya ce dole ne a ci gaba yaki da kungiyoyin yan ta'adda a kasar har zuwa lokacin da za'a tabbatar da cewa babu wani daga cikinsu da ya rage.
Adil Abdul-Mahdi ya bayyana cewa aikin sojojin kasar shi ne tabbatar da tsaron mutane, sannan sadaukar da kai da suka yi ne ya kai ga nasororinn da aka samu kan kungiyoyin yan ta'adda a kasar.
A shekara ta 2014 ne kungiyar yan ta'adda ta Daesh tare da taimakon wasu gwamnatocin kasashen waje da kuma wasu mutane na cikin gida suka mamaye yankunan masu yawa a arewa da kuma yammacin kasar Iraqi, suka kuma shimfadi ikonsu a wadannan yankuna, sannan suka aikata laifuffukan yaki da baya sifantuwa.
Kungiyar Daesh dai, a farko-farkon mamayar kasar ta Iraqi tana da manufar mamaye dukkan kasar ne, amma tare da farkawar malaman addini kan wannan manufar sun hada kai tare da gwamnatin kasar, inda suka bukaci mabiyansu, su shiga yaki da kungiyar Daesh, kafada -da-kafata da sojojin kasar, har zuwa lokacinda aka sami nasara dawo da ikon gwamnatin kasar a dukkan yankunan da kungiyar ta mamaye.
Hadinkai, wanda sojojin kasar ta Iraqi suka yi da mayakan sa kai, wadanda suke cikin kungiyar "Hashdushaabi" wacce aka kafa a ranar 10 ga watan Yunin shekara ta 2014, tare da umurnin manya-manyan malaman addini na kasar Musamman Aya. Aliyu Sistani, sun zama katanga mai karfi wacce ta hana kungiyar Daesh kutsawa cikin sauran yankunan kasar ta Iraqi.
Hadinkai tsakanin gwamnatin kasar Iraqi, sojojin kasar ta kuma mayakan "Hashdusshabi" , har'ila yau ya kai ga nasara aka samu na dawo da ikon gwamnati a kan kungiyar ta Daesh a karshen shekara ta 2017 zuwa farkon shekara ta 2018 da muke ciki.
Sai dai duk da haka, wannan ba ya nuna cewa babu sauran mayakan na Daesh a boye a wasu wurare a cikin kasar ta Iraqi ba. Don har yanzun suna bullowa nan da can a wasu wurare a cikin kasar inda sukan kai hare-haren kunan bakin wake, tada boma-bomai da kuma kashe mutanen ba basu san hawa da sauka ba.
Sai kuma ganin yadda kungiyar ta Daesh take ci gaba da samun taimako da tallafi daga kasashen yamma musamman Amurka da kuma kawayenta na kasashen Larabawa, har yanzun muna iya cewa ba'a kawo karshen kungiyar kwata-kwata ba, Don haka ne sabon Firai minista Adil Abdul Mahdi ya ce marahala ta gaba a yankin da gwamnarin kasar Iraqi take fafatawa da kungiyar Daesh shi yakin leken asiri don gano sauran wuraren da suke boye a cikin a cikin kasar, don wargaza su.