Yemen : Duniya Ta Damu Kan Halin Da Ake Ciki A Hodeida
Kasashen Biritaniya da Faransa da kuma Amurka sun nuna damuwa kan halin da ake ciki a birnin Hodeida da ya kunshi tashar ruwa a yammacin kasar Yemen.
Rahotanni sun nuna cewa a cikin sa’o'i 24, mutane akalla 149 suka mutu a kazamin fadan da ke gudana tsakanin dakarun gwamnatin Yemen da kawancen da Saudiyya ke jagoranta kuma 'yan gwagwamayar neman sauyi na Houthi a garin na Hodeida.
Ministocin harkokin wajen kasashen Biritaniya da Faransa da kuma Amurka sun bukaci bangarorin da su gaggauta kawo karshen faden, da kuma bude tattaunawa cikin gaggawa.
Dama kafin hakan babban sakatare na MDD, Antonio Guterres, ya nuna damuwa matuka kan halin da yankin na Hodeida dake zaman wata hanya ta galibin tallafin da ake shigar dashi kasar zai iya fadawa sakamakon fadan da ake ci gaba da gwabzawa.
Bayanai dai sun nuna cewa kokarin karbe iko da birnin Hodeida mai tashar jiragen ruwa ya gamu da tirjiya sosai daga 'yan Houtsis dake iko da shi.