Sojojin Syria Sun Jaddada Tabbatar Da Tsaro A Garin Minbaj
Majiyar sojan kasar ta Syria ta fitar da sanarwa da a ciki ta tabbatar da cewa za ta tabbatar da tsaron dukkanin mazauna garin Minbaj
A jiya juma'a ne dai sojojin kasar ta Syria su ka sanar da shiga garin na Minbaj tare da daga tutar kasar a cikinsa
Bayan shigar sojojin na Syria cikin garin na Minbaj mazaunansa da mafi yawancinsu Kurdawa ne sun bazama kan tituna cikin murna
Kakakin kungiyar Kurdawan yankin Jayhan Ahamd wanda ya tababtar da shigar sojojin Syria cikin garin ya kara da cewa; A halin yanzu sojojin na Syria suna kokarin datse duk wata hanya da sojojin Turkiya za su bi domin zuwa garin
Tun a ranar 12 ga watan Disamba ne dai shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urgudan ya sanar da fara kai farmakin sojojin kasarsa a wannan yankin na Kurdawa