An Fitar Yan Ta'adda Wasu Daga Kasar Algeriya
Majiyar labarai ta kasar Algeriya ta bayyana cewa an fitar da yayan kungiyar yan t'adda ta "Dakarun Kubutar da Kasar Sham" daga kasar.
Jaridar kasar Algeriya wacce ake kira -Al-Khabar" ta nakalto Hassan Qasimi shugaban bangaren bakin haure na ma'aikatar cikin gida yana fadar haka a yau Alhamis.
Qasimi ya kara da cewa akwai wasu kasashe a yankin wadanda suke kokarin shigo da yan ta'adda cikin kasar Algeriya tare da amfani da Passport na Jebu. Ya kuma kara da cewa wadannan kasashe suna da hannu wajen samar da kungiyar yan ta'adda ta "Dakarun Kubutar da Kasar Sham" da nufin kifar da gwamnatin kasar Siriya.
Sai kuma jaridar "Assama" ta kasar Siriya ta rubuta a cikin shafinta kan cewa bayan rashin nasaran da kungiyoyin yan ta'adda suka yi a kokarinsu na kifar da gwamnatin kasar Siriya sun kokarin dawo da dakarun nasu zuwa kasashen arewacin Afrika sannan suna shigowa kasar Algeriya ce daga kasashen Mali da Niger.