Harin Bam Ya Yi Ajalin Mutum 3 A Kudancin Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34878-harin_bam_ya_yi_ajalin_mutum_3_a_kudancin_siriya
Rahotanni daga Siriya na nuni da cewa wani harin bam ya yi sanadin mutuwar uku a kudancin Damascos babban birnin kasar.
(last modified 2019-01-20T10:53:19+00:00 )
Jan 20, 2019 10:53 UTC
  • Harin Bam Ya Yi Ajalin Mutum 3 A Kudancin Siriya

Rahotanni daga Siriya na nuni da cewa wani harin bam ya yi sanadin mutuwar uku a kudancin Damascos babban birnin kasar.

Wasu bayanai da kungiyoyi masu zaman kansu suka fitar sun nuna cewa an kai harin ne a cikin wata motar bus a yankin Afrine. 

Kungiyar dake sa ido kan al'ummar kare hakkin bil adama ta OSDH, ta ce bayan harin an kuma karen harbe harben bindiga.

Shi ma dai gidan talabijin din kasar ta Siriya ya kawo labarin aukuwar harin, tare da bayyana hakan a matsayin harin ta'addanci, saidai ba tare da bayyana adadin mutanen da lamarin ya rutsa dasu ba.

Wannan dai kusan shi ne harin farko a birnin Damascos a cikin sama da shekara guda.