Venezuela: An Kame Sojojin Da Su Ka Yi Tawaye
(last modified Tue, 22 Jan 2019 07:28:35 GMT )
Jan 22, 2019 07:28 UTC
  • Venezuela: An Kame Sojojin Da Su Ka Yi Tawaye

Gwmanatin Venezuela ta sanar da kame wasu sojoji 27 da su ka yi tawaye suna masu kiran shugaban kasar Nicolas Maduro da ya yi murabus

Rahtoannin da suka rika fitowa daga kasar ta Venezuela sun tabbatar da cewa; An yi juyin mulkin da bai kai ga samun nasara ba a jiya Litinin

Ma'aikatar tsaron kasar ta Venezuela ta sanar da cewa; An dakile wani hari da aka kai wa sansanin soja da ke cikin babban birnin kasar Caracas tare da kwace makaman da aka sace

Yunkurin juyin mulkin dai ya zo mako guda da kafafen watsa labarun Amurka su ka sanar da cewa; Wahsington tana shirin bayyana jagoran 'yan hamayya a matsayin shugaban kasar Venezuela.

Alaka a tsakanin Amurka da Venezuela ta kara tsami bayan da Donald Trump ya zama shugaban kasar Amurka