An Kafa Gwamnatin Labnon Bayan Watani 9 Da Zabe
Bayan kwashe watani 9 da zabe, a daren jiya Alhamis, an kafa gwamnatin hadakar kasar Labnon bisa jagorancin Firaminista Sa'ad al-Hariri
Firaministan kasar Saad al-Hariri ya kaddamar da gwamnatin hadaka wacce za ta kawo karshen matsalar durkushewar tattalin arziki da kasar ke fuskanta.
Masana a kasar sun yi hasashen cewar sabuwar majalisar zartaswar kasar wacce ta kunshi ministoci 30 daga jam'iyyin adawa za ta fusakanci kalubalen tattalin arziki kasancewar kasar wacce tafi kowacce kasa yawan bashi yanzu, tun bayan bullar rikici a kasar Siriya rashin aikin yi ya karu a Lebanon da kaso 20 tsakanin shekara ta 2011 zuwa shekara ta 2014 lamarin da ya zuwa yanzu gwamnatin ta gagara magancewa.
Kungiyar Hezbollah na daga cikin wacce ta rabauta da mukaman ministoci uku da suka hada da m'aikatar kiyon lafiya, ma'aikar harakokin wassani da ministan mai bayar da shawara kan harakokin Majalisar a cikin sabuwar gwamnatin hadakar.