Mar 05, 2019 04:57 UTC
  • Rashin Zaman Lafiya Ne Ke Karfafa Ta'addanci A Kasashen Larabawa

Kungiyar kasashen Larabawa ta bayyana rashin zaman lafiya a wasu kasashe mambobinta, ne ke kara karfafa ayyukan ta'addanci musamman na kungiyar Da'esh a yankin.

Babban sakataren kungiyar ne, Ahmed Aboul Gheit, ya bayyana hakan, a yayin taron ministocin shari'a da na cikin gida na kungiyar da ya gudana a ranar Litini a birnin Tunis.

Taron na Tunis wanda shi ne irinsa na uku, ya maida hankali ne wajen kan hada kan kasashen larabawan, da kuma bukatar hadin guiwa tsakaninsu wajen yaki da muggan laifuka.

Sanarwar karshen taron kasahen larabawan ta ce, ta'addanci shi ne babban kalubalen da ke a gabansu, duk da cewa ta yaba da yadda aka karya laggon kungiyoyin yan ta'addan a baya bayan nan.

A yayin taron, kasashen sun cimma yarjejeniya guda biyu da suka shafi yaki da safara mutane, da yaki da safara da sassan jikin mutane.

Sai dai ministocin cikin gida na kasashen da suka hada da na kasashen Aljeriya, Masar, Qatar, Kowait da kuma Yemen basu halarci taron ba.

 

 

 

Tags