An Bukaci Dage Zaben Shugaban Kasa A Kasar Aljeriya
Jam'iyyun adawa a kasar Aljeriya sun bukaci a dade zaben shugaban kasar wanda aka shirya gudanarwa a cikin watan Afrilu na wannan shekara.
Tashar talabijin ta Sky News ta nakalto wani bayanin da jam'iyyun adawar suka fitar wanda yake bukatar a dage zaben shugaban kasar kamar yadda ayar doka ta 102 ta kundin tsarin mulkin kasar ta ayyana, musamman idan an shiga irin halin da ake ciki a kasar.
Bayanin ya kara da cewa jam'iyyun adawan sun ce basu amince da shiga takarar shugabancin kasar na shugaban Abdulazizi Butaflika ba, sannan basu amince da zancensa a wani jawabin da yayi a cikin yan kwanakin da suka gabata ba.
Bayanin ya kara da cewa idan ba'a dage zabenba, ko kuma shugaba Abdulaziz ya ki janyewa daga takararsa na shugabancin kasar a karo na 5 ba, mai yuwar kasa ta fadi cikin tashe-tashenn hankula masu tsanani.
Banda haka jam'iyyun adawar sun nuna goyon bayansu ga zanga-zangar da mutanen kasar suke yi na rashin amincewarsu da bukatar shugaban kasar na shiga takarar shugabancin kasar karo na biyar.
A jawabin da shugaba Butaflika yayi dai, bayyana cewa, idan an gudanar da zabe, kuma shi ne ya lashe shi, to zai sauka daga kan kujerar shugabacin kasar.