Wakilin MDD Kan Rikicin Syria Ya Isa Damascos
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i3736-wakilin_mdd_kan_rikicin_syria_ya_isa_damascos
Wakilin MDD kan rikicin kasar Syria, Staffan de Mistura ya isa birnin Damascos domin ganawa da mahukuntan kasar akan tattaunawar Geneva.
(last modified 2018-08-22T06:58:07+00:00 )
Apr 11, 2016 00:26 UTC
  • Staffan de Mistura, mai shiga tsakani a rikicin Syria (hoto rumbun ajiya ws.irib.ir/)
    Staffan de Mistura, mai shiga tsakani a rikicin Syria (hoto rumbun ajiya ws.irib.ir/)

Wakilin MDD kan rikicin kasar Syria, Staffan de Mistura ya isa birnin Damascos domin ganawa da mahukuntan kasar akan tattaunawar Geneva.

A makon daya gabata ne Mr De Mistura ya sanar cewa zai kai wata ziyara a kasashen Syria da Iran daya daga cikin kasashen dake da fada aji a yunkurin samar da zamen lafiya a Syria.

Mr De- Mistura ya bayana cewa yana son ganawa da dukkan masu ruwa da tsaki a rikicin Syria da nufin kusanto su akan jadawalin kafa gwamnatin wucin gadi ta siyasa a Syria, kafin tattauanawar ta Geneva ta biyu.

An dai yi tattaunawar farko ce a ranar 24 ga watan Maris daya gabata, sanan a yau 11 ga wata Afrilu aka shirya yin tattaunawar ta biyu, saidai aka dage ta har 13 ga watan nan.