Syria : Jama'a Sun Fito Sosai A Zaben 'Yan Majalisar Dokoki
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i3844-syria_jama'a_sun_fito_sosai_a_zaben_'yan_majalisar_dokoki
Rahotanni daga Syria na cewa an samu fitowar masu kada kuri'a yadda ya kamata a yayin zaben 'yan majalisar dokokin kasar na yau laraba.
(last modified 2018-08-22T06:58:07+00:00 )
Apr 13, 2016 13:09 UTC
  • fira ministan Syria Waël Halaqi.
    fira ministan Syria Waël Halaqi.

Rahotanni daga Syria na cewa an samu fitowar masu kada kuri'a yadda ya kamata a yayin zaben 'yan majalisar dokokin kasar na yau laraba.

'yan takara fiye da dubu 3 ne ke neman wakilici a majalisar dokokin kasar mai kujeru 250.

Jim kadan bayan ya kada kuri'a firaministan kasar Waël Halaqi ya bayanawa manema labarai cewa wannan rana ce mai cike da tarihi ga Syria, inda al'umma kasar ke zabar wakilan su bisa tafarkin demukuradiyya domin shafe masu hawayensu.

kazalika a cewar Mr Halaqi wannan na zuwa ne a daidai lokacin dakarun kasar ke ci gaba da samun galaba a yakin da suke da 'yan ta'ada da sukayi kaka-gida a sassa daban-daban na kasar.

Zaben dai na yau ya zo ne a daidai lokacin da aka fara taron samar da makoma ga kasar Syria wanda ke gudana a birnin Geneva karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya.

Saidai masu hamayya da shugaba Bashar Assad da kuma kasashen da ke mara masu baya na kallon zaben na yau a matsayin wanda ba ya da wata kima.