Ci gaban sojojin Siriya wajen tsarkake ganin Halab.
Dakarun tsaron Siriya da Dakarun sa kai sun samu nasarar tsarkake wani bangare na gefen arewacin jihar Halab
Kamfanin dillancin Labaran kasar Siriya Sana ya habarta ce A yau Alkhamis Dakarun tsaron kasar da na sa kai sun samun nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama a sansanin Handarat dake gefen arewacin jihar Halab tare da tsarkake wannan yanki daga 'yan ta'addan.
A bangare guda jiragen yakin Siriyan sun kai hare-hare ta sama a tunkar 'yan ta'addar dake yankin Addamir da gabashin tashar wutar lantarki naTashrin dake gefen garin Damuscus tare da hallaka 'yan ta'adda da dama, har ila yau Dakarun tsaron na Siriya sun samu nasarar dakille wani harin 'yan ta'adda a wasu kauyuka dake gabashin na Halab. a wani harin da 'yan ta'addar suka kai yankunan fararen hula a garin na Halab, yayi sanadin jikkata wani adadi na fararen hular, daga cikin su har wasu Mata da kananen yara.
Tun daga ranar 27 ga watan Favrayun da ya gabata ne yarjejjeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a kasar Siriyan, saidai wannan yarjejjiya ba ta shafi kungiyoyin 'yan ta'adda irin su ISIS da Jabhatu Nusra.
Ajiya laraba ne aka sake buda taron tattaunawar sulhu bisa shiga tsakanin Majalisar Dinkin Duniya a birnin Ganeva.